Hausa WASSCE (SC), 2016

Question 7

(a)  Mene ne jigon wakokin makadan dambe da na ‘yan tauri
(b)  Yi takaitaccen bayanin makadan dambe da na ‘yan tauri

 

Observation

Above is a question from the book Kowa Ya Sha Kiɗa (Oral poetry). Candidates were required to mention the theme of the songs composed for traditional boxers and ‘yan tauri

Thus:
(a) Jigon waƙoƙin makaɗan ’yan tauri da na dambe shi ne zuga (koɗa mutum)
(b)  i.  Makaɗan dambe
Ɗambe yana daga cikin wasannin gargajiya na Hausawa wanda, aka fi yi da
kaka. Masu sha‘awar dambe sukan haɗu su tsayar da ranar da za a yi.  Idan
ranar ta kusa, sai ‘yan dambe su yi ta haɗuwa a garin, kowa da makaɗinsa.
Idan an zo filin damben, sai kowane maƙaɗi ya dinga zuga ɗan dambensa.
Misalin makaɗin dambe shi ne Ɗan’anace.

ii. Makaɗan ‘yan tauri
Su ma ‘yan tauri, wasu mutane ne, waɗanda suke da’awar su jarumai ne
masu maganin ƙarfe da sauran dukkanin makamai. Sukan yi da’awar yin
abin da ba kowane mutum zai iya ba, kamar shiga ramin kura a ɗauko ’ya’yanta.  Su ma suna da makaɗa da suke zuga su. Misali : Alhaji
Hamisu Sarkin Kiɗa na Kano da Kassu Zurmi da sauransu.

 

Candidates’ performance on this question was fair.