Hausa WASSCE (SC), 2016

Question 13

Bayyana yadda bikin hawan daba.

Observation

This question is on tradition and the candidates were expected to explain how daba (riding of horses during festival or entertainment of a special guest) is done.

 

Thus:
Hawan daba biki ne wanda sarakuna suke haɗuwa don sada zumunci da ƙara ƙulla shi a junansu.  Yawanci, akan yi taron daba ne da nufin taryen wani babban mutum, ko wani babban baƙo na nesa, da makamantansu.  Bikin hawan daba an faro shi ne bayan zuwan Turawa wannan ƙasa ta Hausa da Nijeriya baki ɗaya. Bikin daba hawa ne na dawaki da kowane sarki ko hakimi yake haɗa ƙungiyarsa su hau dawaki, bayan an yi wa dawakin nan kwalliya iri-iri kowane sarki da tawagarsa zai zo ya zagaya filin da aka shirya don bikin. Babban muhimumin abin da bikin daba yake nunawa, shi ne nuna kyawawan  al’adun Hausawa, waɗanda suka shafi sutura da ire-iren ƙawa da nuna jaruntaka,kamar farauta da yaƙe-yaƙe. d. s.

 

Candidates’ performance on this question was good.