Hausa WASSCE (SC), 2016

Question 4

Kawo sigogi uku na jinsin mace tare da misalai hudu-hudu na kowanne.

 

Observation

The question above is on grammar, and candidates were required to list three ways by which feminine gender could be identified and to give four examples each.

Sigogin jinsin mace:
(a) ɗafin:
i.  -iya, misali:  bebiya, baturiya, jakadiya, itaciya, malalaciya, maƙaryaciya, d.s.
ii.  -anya, misali:  zakanya, zomanya, biranya,  ƙatanya,   bokanya, d.s.
iii. -uwa, misali:   tsuntsuwa, tsohuwa, baƙuwa, zabuwa, doguwa, gurguwa, muguwa, d.s.

 

(b) Sunayen mata, misali:  Binta, Lami, Indo, Jummai, Talatu, Hauwa, Aisha, d.s.
(c) Sunayen ƙasashe misali:  Nijeriya, Birtaniya, Ghana, Sudan, Amurka,
Faransa, Indiya, d.s.

(d) Sunayen ranaku misali:  Lahadi, Litinin, Talata, Laraba, Alhamis, Juma’a, Asabar.

 

Many candidates attempted the question and their performance was encouraging.