SECTION C
CUSTOMS AND INSTITUTIONS
Question 12
Bayyana aikin biyar daga cikin waɗannan:
- Sarkin gida
- Shamaki
- Sallama
- Sarkin ƙofa
- Baraya
- Uwar soro
- Jakadiya
Observation
Candidates were required to explain any five (5) palace title holders listed in the question. The following explanations should be considered as relevant:
(a) Sarkin gida:
Yana zama kusa da barayar sarki;
Yana da damar shiga ko’ina a cikin gidan sarki.
(b) Shamaki:
Yana yi wa mutane iso ga sarki;
Yana yi wa sarki zagi idan zai fito daga cikin gida.
(c)Sallama:
Yana isar da gaisuwar talakawa zuwa ga sarki;
isar da kyautar sarki zuwa ga talakawa.
(d) Sarkin ƙofa:
Yana tsaron ƙofar gidan sarki;
Yana da ikon hana shiga ko fita daga ƙofar gidan sarki.
(e) Baraya:
Yana da alhakin kula da barayar sarki;
Yana da alhakin kula da abin da duk ya shafi shimfiɗun sarauta da tufafi da abincin sarki.
(f) Uwar soro:
Matar da take iya faɗa wa sarki abin da ake jin nauyi ko shakkar faɗa masa, ita ce uwar soro. Tana iya kasancewa ɗaya daga cikin waɗannan matan:
Mahaifiyar sarki;
Yayar sarki;
Gwaggon sarki;
Uwargidan sarki (matar fari).
(g) Jakadiya:
Jakadiya mace ce wadda take da alhakin:
Isar da saƙon sarki zuwa ga iyalinsa;
Isar da saƙon iyalin sarki zuwa ga sarkin;
Isar da saƙon sarki ko na iyalinsa ga wasu mutane na waje.
Candidates who attempted this question performed very well.