Question 5
(a)Mene ne a’antawa
(b)Kawo misali uku na waɗannan a’antawar:
(i) ta gabaɗaya
(ii) ta lokuta da waninsu
(iii) ta sarƙaƙƙiyar sifa
Observation
The question is also on grammar and candidates were required to explain negation in (a) and give three examples from each type of negation listed in (b). The answer should be as follows:
(a) A’antawa tana nufin a’a ko kuma kore ma’anar zance daga “i” zuwa “a’a”.
Misali:
Aliyu ya zo.
(Ana iya a’anta shi zuwa)
Aliyu bai zo ba.
(b) i. Ta gaba ɗaya:
Ana amfani da a’antau ba .......... ba.
Misali:
Audu yaro ne = Audu ba yaro ne ba
jakar baƙa ce = jakar ba baƙa ce ba
yaran manya ne = yaran ba manya ne ba
Iliya malami ne = Iliya ba malami ne ba
gidan ya lalace = gidan bai lalace ba
kafin ku zo = ba kafin ku zo ba
biyar = ba biyar ba
ii. Ta lokuta da waninsu:
Misali:
ka rubuta = ba ka rubuta ba
káà rubuta = ba káà rubuta ba
kà faɗa = kada ka faɗa
ta zo = ba ta zo ba
sun tafi = ba su tafi ba
ya zo = ba ya zo ba
nakan ci = ba nakan ci ba
suna shiga = ba su shiga
za ka rubuta = ba za ka rubuta ba
ii. Ta sarƙaƙƙiyar sifa:
Misali:
mai gida = maras gida
mai haƙuri = maras haƙuri
mai ƙoƙari = maras ƙoƙari
masu gida = marasa gida
masu hankali = marasa hankali
mai iko = maras iko
Many candidates attempted the question and their performance was encouraging.