Question 13
- Mene ne su?
- Yi bayanin yadda ake yin su ta waɗannan hanyoyi:
(i) Fatsa
(ii) Lalube
(iii) kwalfe
Observation
Candidates were required to explain ‘Su’(fishing) in (a) and explain the methods of fishing listed in (b). The following explanations should be considered as relevant:
(a) Su:
Su sana’a ce ta kamun kifi wadda Hausawa suke yi domin samun abin masarufi don tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum. Sana’a ce wadda ake gadonta kamar sauran sana’o’in Hausawa nagargajiya.
(b) i. Fatsa:
Hanya ce ta yin su ta amfani da ƙugiya da lilo wanda za a liƙa wani abinci kamar kitse ko tana ko tsutsa. Sannan a ɗaura ƙugiyar a jikin sanda mai ƙarfi, wadda mai yin fatsa zai rike. A tsakanin lilon da ƙugiyar akan ɗaura kara ko toto (totuwar masara) domin nuna alamar taɓi.
ii. Lalube:
Hanya ce ta kamun kifi da hannu.
iii. Kwalfe:
Hanya ce ta kamun kifi wadda ake kwashe ko kwalfe ruwan da aka datse ko aka killace.
Candidates’ performance on this question was very good