Question 7
Yi bayaninasalin samuwar waƙa ta hanyar bautar iskoki da dodanni.
Observation
Above is a question on the book Jagoran Nazarin Waƙar Baka (Oral Poetry). Candidates were required to give an account on how oral songs were originated from the worship of demons and monsters. The candidates’ response should be as follows:
Gabatarwa:
Ma’anar waƙa;
Bayanin ra’o’in masana game da asalin waƙa.
Gundarin jawabi:
Bautar iskoki;
Bukukuwan shekara;
Kirari, zuga, kambamawa;
Kaɗa take;
Yanke-yanke da shaye-shaye.
Kirarin Tsumburbura da Barbushe:
Jamuna, akasa, mun gama,
Ga Tsumburbura kanawa,
Ga Magajin dala.
Amshin Barbushe:
Ni ne magajin Dala,
Da kun ƙi da kun so,
Ku bi ni ba ra’i ba.
Kirarin dodo Na Kyauka:
Dodo maye,
Dodo na ba kashi,
Kashe mutum mu tai gida,
Dodo na ba kashi,
Dodo ɗan doguwa,
Dodo na ba kashi,
Birkiɗi ba kyakya.
Kirarin Inna Bafillatana:
Mai gambara ina wata kama,
Mai ɗan zane ta Baushe,
Mai ɗan zane Iya,
Kaluluwa ta Baushe,
Shagiɗai-shagiɗai na gan ta,
Mangarai-mangarai na gan ta,
Karkatai-karkatai na gan ta.
Kammalawa:
Yin taƙaitaccen bayani a kan muhimman batutuwan da aka tattauna a kai.
Candidates’ performance on this question was fair.