Hausa Nov/Dec 2015

Question 10

    Shin kam akwai wata daukaka ko ci gaba,
              In ba sani daidai da kwayar zarra?

              A takaice amsa ‘babu’,shi ne ginshiki,
    Duk wanda zai yi gini a kai zai dora.

    (a) Daga wace waka aka ciro wadannan baitoci?
    (b) Mene ne jigon wakar?
    (c) Bayyana wadannan baitoci a takaice.


Observation

The stanzas above were taken from the book Ciza Ka Busa (Written poetry) and the candidates were expected to identify the song where the stanzas were taken, the theme of the song and to explain the stanzas.
Thus:
             
10.     (a)      An ciro waɗannan baitoci daga waƙar ‘Mu aikata gaskiya ‘yan dara.
(b)     Jigon waƙar shi ne gargaɗi.
(c)      Waɗannan baitoci gargaɗi suke yi wa irin mutanen nan waɗanda basu san komai
            ba game da addininsu ko ilimin zamani, amma suna fankama suna yaudarar 
 kansu cewa su wasu manyan mutane ne. Marubucin ya jawo hankalinsu ta hanyar nuna masu cewa mutum ba shi da wata ɗaukaka ko wani ci gaba in dai ba shi da ilimi domin shi ne ginshiƙin da za a ɗora abubuwa a kai.

           Candidates performance on this question was not encouraging.