Hausa Nov/Dec 2015

Question 6

    Yi takaitaccen bayanin yadda ake yin wasan Dan Dukushi

Observation

The question above was taken from the book Labarun Gayagiya 2 and the candidates were expected to explain briefly how the play Dan Dukushi is staged.

Thus:

Yara maza ne ke yin da’ira a kama hannuwa da kyau. Daga nan sai ɗaya ya saki hannunsa, ya yi matakala da tafin hannunsa na hagu a guiwar ƙafarsa ta hagu. Sai yaro na hagu da shi ya taka matakalar nan da ƙafarsa ta hagu, ya ɗago ƙafarsa ta dama ya tsallake kan wanda ya taka wa hannu, ya dire ƙasa. Shi kuma na dama da shi ɗin, na dama da shi ya yi masa haka ya taka ya dire, har a zagayo ana waƙa, kamar haka:
Bayarwa:       Ɗan duƙushi
Amshi:          Hiyya
Bayarwa:       Warwarwar
Amshi:          Hiyya
Bayarwa:       Ba shi ruwa
Amshi:          Hiyya
Bayarwa:       Kamar na me?
Amshi:          Hiyya
Bayarwa: dokin naka ƙuru ne ba ka ba shi ruwa da ciyawa ba.

          Haka za a yi ta yin waƙa ana hawa ana direwa har wasan ya zagayo.

          The performance of candidates on this question was not encouraging.