Hausa Nov/Dec 2015

Question 12

                Bayyana yadda ake reno daga haihuwa har zuwa lokacin da yaro ya fara zama.


Observation

The question above is on Customs and Institutions (Al’ada). Candidates were required to explain the processes of nursing a baby from birth to the period of weaning.
Thus:
Bayan haihuwa, uwar jinjiri za ta ci gaba da shayar da shi nononta. Shi ne     muhimmin abincinsa. Shi zai ci gaba da sha har lokacin yaye. Ba za a fara ba jinjiri kowane irin abinci basai ya kai kimanin wata shida, sannan a riƙa dama kunun hatsi ana ba shi, sau da yawa, akan yi masa ɗure ne, domin bai saba ba, a hankali har ya san daɗinsa.
Da zarar ya kai wata takwas ko goma sai a fara ba shi abinci, amma maras barkono. A hankali a hankali har ya fara ci da kansa, duk da kasancewa yaro ya fara cin abinci, duk lokacin da ya bukaci nonon mahaifiyarsa, sai ya sha.
Lokacin da yaro ya kai wata biyar ne, za a fara koya masa zama. Kafin ya kai wata bakwai kuma, ya fara rarrafe, a wannan lokacin kuma, zai fara kamuwa da yawan zazzabi da gudawa. Wannan ita ce alamar fitar haƙora. Duk da haka, zai ci gaba da shan nonon mahaifiyarsa tare da kunu da abinci maras yaji.

Candidates’ performance on this question was encouraging.