Hausa Nov/Dec 2015

Question 13

    Bayyana yanayin aikin wadannan:
              (a)      Mai’unguwa;
              (b)     Hakimi.


Observation

This question is also on Customs and Institutions and the candidates were expected to explainthe roles of Mai’unguwa and Hakimi in Hausa culture.

Thus:
(a)      Mai’unguwa
Shi ne yake yin sulhu da sasamta jama’a idan wata rigima ta taso, musamman rigimar gona, ko ta aure ko faɗa, da makamantansu. Shi ne hukuma a unguwarsa, don kuwa shi ne shugaba kuma wakilin hukuma. Dukkan abin da hukuma za ta yi, sai ta sanar da shi, ta nemi goyan baya da taimakonsa.

(b)     Hakimi
Shi ne shugaban gari ko ƙasa wanda ƙauyukan dagatai suke ƙarƙashinsa. Shi ne yake kula da ƙauyukan yankin ƙasarsa. Duk abin da hukuma take bukatar jama’a ta yi, sai ta aiko ta wajen hakimi, shi kuma ya tara dagatai da masu unguwanninsa ya ba su umurni. Shi ne mai kwantar da duk wata rigima ko tarzoma da ta tashi a ƙasarsa. Shi ne mai yin shari’a ya sasanta jama’a game da wasu matsaloli. Shi ne wakilin hukuma mai hakkin kula da zaman lafiyar kasarsa.

                             Candidates’ performance on this question was encouraging.